A jiya Litinin ne majalisar dokokin jihar kano ta yi wa dokar da za ta tabbatar da daurin rai da rai ga dukkan wanda aka samu da laifin satar mutane don yin garkuwa da su wato (KIDNAPPING) karatu na biyu a harabar majalisar, wanda mataimakin shugaban amsu rinjaye na majalisar Alhaji Maifada Bello ne ya gabatar da kudurin.
Dan majalisar da ke wakiltar karamar Hukumar Kibiya, ya bayyana cewar akwai bukatar majalisar ta gaggauta sanya hannu akan wannann doka a jihar kano wanda hakan zai baiwa alkalan jihar dammar yanke hukuncin akan wadanda aka kama da shaidu a fili da wannan mummunar sana’a ta sace mutane domin karbar kudin fansa, kuma wanda galibi bincike ya gano cewar daga kana nan yara sai tsofaffi da mata hakan ke faruwa da su.
Ya ce dokar da ta tabbatar da hukunci akan masu satar mutane an samar da ita ne tun shekarar 1963, duba da haka akwai bukata a sake gyarata da tabbatar da daurin rai da rai ga duk mutumin da aka samu ya aikata hakan, musamman la’akari da yadda wannan mummunar dabi’a ta satar mutane a nan jihar kano kullum ke kara yawaita, musamman a bangaren arewacin jihar kano, alafazin dan majalisar dokin jihar Kano Maifada Bello.
Ya ci gaba da cewa, hakan zai taimaka tare da rage wa alkalan wahalar da suke fuskanta na yanke hukunci akan masu irin wannan laifi, wanda shekaru 10 ne kadai dokar a yanzu ta tanadarwa masu aikata wannan laifi, wanda ba karamar wahala alkalan ke sha ba wajen aiwatar da shi a halin yanzu.
Wannan doka a cewar Maifada, za ta taimaka baiwa masu aikata wannan laifi zabi biyu kacal, ko dai su tuba su daina ko kuwa doka ta yi tsaiwar wata akansu ba tare da nuna sanayya ba, dan kuwa haka doka take, wanda cewar Maifada su a matakin majalisa za su yi duk abinda ya kamata wajen tabbatarwa wannan doka ta tabbata.