Jihar Kano Zata Ta Fara tara Naira Bilyan 10 na kudin shiga Duk Wata – Ganduje


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce Gwamnatinsa ta kuduri aniyar tara milyan dubu sau dubu Goma a matsayin kudaden shiga duk wata a jihar. 
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar din da ta gabata a wajen laccar bitar aiki na kwanaki uku da jam’iyyar APC ta shiryawa shuwagabanni da masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar Kano. 
Ganduje ya ce a lokacin da ya karbi mulki a 2015 jihar na tara milyan N500 zuwa Milyan N600 ne a duk wata a matsyin kudaden shiga, amma bayan hawansa yanzu jihar na samun milyan dubu sau dubu Uku duk wata kuma duk da haka suna neman kari.
Yana mai cewa kawo yanzu majalisar dokokin jihar na bitar dokokin samun kudaden shiga daban-daban na jihar domin habbakasu.
Sai dai yace Gwamnati ba zata dauki duk wani mataki da zai kuntatawa jama’a ba. Yana mai cewa abun jin dadi shine yadda  Al’ummar jihar ke biyan kudaden haraji a kashin kansu saboda sun gamsu da yadda ake kashe kudaden nasu.
Gwamnan yace ana amfani da kudaden harajin ne wajen gudanar da wasu manyan ayyuka na musamman da suke kyautata rayuwar jama’ar jihar. 
“Muna sanya alama a duk wani aiki da muka yi amfani da kudaden haraji wajen aiwatar da shi” inji shi 
Sannan Gwamnan ya kuma yi alkawarin cigaba da jan ragamar jihar a bisa adalci da amana da tsoron Allah da nuna kwarewa domin daga darajar jihar da Al’ummarta.

You may also like