Jihar Kebbi za ta iya samar da kaso 50 na shinkafar da kasarnan ke bukata da cigaban shirin Gwamnatin Tarayya na tallafin noma, a cewar Garba Dandiga kwamishinan noma na jihar.
Dandiga ya bayyana haka lokacin da yake zagawa da wata tawagar yan jaridu domin duba shirin noman shinkafa na FADAMA dake Suru.
Gonakin da ake noma shinkafa karkashin shirin sun kai tsayin Kilomita 50 da kuma fadin Kilomita 20.
Ya ce kananan hukumomi 16 suna noman shinkafa sosai a jihar ya yin da miliyoyin matasa da kuma yan fansho suka tsunduma harkar noma.
Kwamishinan ya ce musamman da ake san ran samun kaka mai kyau a shekarar 2018 gonakin Fadama dake Suru za su iya samar da shinkafa sanfera tan miliyan 2.5.
Ya ce a shekarar 2017 tan miliyan 1.5 na shinkafa aka girbe a gonakin dake Suru.
Kwamishinan ya ce domin bunkasa samar da shinkafar, gwamnati ta sayo motocin noma iri daban-daban guda 900 domin tallafawa manoman.