Jihar Ogun ce ke kan gaba da yawan mutane da Buhari ya nada kan mukamai


Da mukamai 21 jihar Ogun ce ke kan gaba da yawan mutanen da shugaba Buhari ya bawa mukamai tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

 Femi Adesina mai magana da yawun shugaban kasa shine yafitar da jerin mukamai 159 wanda shugaban kasar ya nada,  da yammacin ranar Asabar.

Jihohin Imo, Kano, Katsina da kuma Edo  sune ke  biye  mata baya da mukamai 14.

Kaduna tana da 12, Adamawa da Bauchi suna da 11,yayin da Lagos take da 10.

Benue, Delta,Niger, da kuma Osun suna da 9 kowaccensu, Gombe da Jigawa suna da 8, Jihar Rivers na da 7 yayin da Bayelsa da Ondo suke da 6.

Cross River, Nassarawa, Plateau, Taraba da kuma Yobe kowaccensu na da mukamai biyar, Enugu, Ekiti, Akwa Ibom, Oyo, Sokoto da Zamfara suna da 4 kowaccensu, Kebbi na da 3 yayin da jihohin Abia da Ebonyi suke da mukamai bibiyu.

Fadar shugaban kasa ta sakin jerin yawan nade-naden mukaman ne a matsayin martani kan wani rahoto da yayi zargin cewa Buhari yafi bada fifiko kan yan arewa a mutanen da yake nadawa akan  mukamai


Like it? Share with your friends!

0

You may also like