Jihar Sokoto Zata Soma Amfani Da Wutar Lantarki Mallakar JiharGwamnatin jihar Sakkwato a karkashin jagoranci Aminu Waziri Tambuwal, ta dauki matakan ganin an soma amfana da wutar lantanki a jihar, Wanda aka dauki matakan gwaje-gwajen a dukkanin Injimukkan dake wurin, abinda kawai ya rage shi ne amincewar hukumar bada wutar lantarki ta kasa.
Da yake bayani a lokacin, da yake duba aikin gwajin, Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Bashir Garba, ya bayyana wa manema labarai cewa, kasancewa wutar da ake amfani da ita a Nijeriya, ba ta wadatar da al’ummar kasa, wanda ya zama dalilin Gwamnatin jihar Sakkwato ta yi tsaye daka a wajen ganin an kammala aikin samar da wutar lantarki mallakar jihar.
Farfesa Bashir Garba ya kara da cewa, aikin zai samar da karin, mega talatin da takwas ga al’ummar jihar ta Sakkwato idan ya fara aiki, wanda a halin yanzu aikin ya yi nisa, abin da ya rage a hada wutar da hukumar samar da wuta ta kasa, domin rarrabawa ga wuraren da ya dace.
Ya bayyana cewa, aikin da aka yi nan bada dade wa ba, jihar Sakkwato za ta rika samun wuta a tsawon awa ashirin da hudu.

You may also like