Jihohi 35 sun samu bashin biliyan ₦29  su biya albashi


Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a  saki kuɗi biliyan ₦29 a matsayin bashin tallafin kasafin kuɗi ga jihohi 35 banda jihar Lagos wacce ba ta bukatar tallafin bashin.

Udom Udoma, Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare ya bayyana haka ga manema labarai a karshen taron majalisar dake lura da tattalin arzikin kasa wacce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ke jagoranta.

A cewarsa kowacce jiha za ta karbi miliyan ₦800 domin cika kuɗin biyan albashi, fansho da kuma sauran bukatu.

Udoma yace shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi umarni a sakarwa jihohin kuɗin ta ofishin babban akanta na kasa.

Ya ce gwamnonin 35 sun nuna godiyarsu ga shugaban kasa Buhari kan bashin kuɗin da aka basu.

You may also like