Jihohi shida da suka koma hannun ƴan adawa a NajeriyaBBC

Duk da cewa har yanzu ba a kammala bayyana sakamakon zaɓen jihohi 28 cikin 36 da aka yi a Najeriya ba a ranar 18 ga watan Maris, amma ya zuwa yanzu akwai wasu jihohi da ƴan adawa suka karɓe daga hannun masu mulki.

Zuwa yanzu jihohi shida sun koma hannun jam’iyyun adawa waɗanda suka haɗa da Benue da Cross Rivers da Kano da Sokoto da Plateau da kuma Zamfara.

Amma jiran tsammani a wasu jihohin da suka haɗa da Adamawa da Abia da Kebbi da Enugu ka iya ƙara yawan waɗannan jihohin da shida.

Samun nasara kan jam’iyyar da ke mulki a Najeriya wani abu ne mai cike da mamaki, masana na ganin babu ɗan hamayyar da zai iya ƙwace mulki da tazarar da ba ta kai ta kawo ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like