
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa a Najeriya na ƙarasa zaɓuka kusan 100 da suka rage, ciki har da na gwamnoni a jihohin Kebbi da Adamawa.
An bayyana zaɓukan a matsayin waɗanda ba su kammala ba ne, lokacin babban zaɓe na ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma na ranar 18 ga watan Maris.
Baya ga zaɓen gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi, za kuma a kammala zaɓukan ‘yan majalisar dattijai guda biyar da na ‘yan majalisar wakilai 31.
Akwai kuma zaɓukan ‘yan majalisun dokoki na jihohi guda 58 da ake ƙarasawa duk a yau Asabar.
INEC ta ce tuni aka kammala zaɓukan gwamnoni a jihohin Najeriya 26, da na ‘yan majalisar dattijai 104, sai kuma ‘yan majalisar wakilai guda 329, da zabukan ‘yan majalisun dokokin jihohi 935, tuni kuma aka ayyana waɗanda suka yi nasara.
Akasari dai, an soke zaɓukan tasoshin da ake kammalawa yau Asabar ne saboda tashe-tashen hankula da hargitsa zaɓe da kuma sauran matsaloli.
A ina ake ƙarasa zaɓukan?
A jihar Adamawa, ana kammala zaɓen gwamna tsakanin manyan jam’iyyu guda biyu, wato PDP da kuma APC.
Masu zaɓe 37, 706 ne ake sa rai za su kaɗa ƙuri’u a tashoshin zaɓe 69 cikin ƙananan hukumomin jihar 20.
A zaɓen ranar 18 ga watan Maris, INEC ta bayyana gwamna mai ci Ahmadu Umar Fintiri da cewa ya samu ƙuri’a 421,524.
Sai babbar abokiyar fafatawarsa ta jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a 390,275.
Ita ce mace ta farko da ta taɓa zuwa wannan matakina zaɓen da za a kammala a takarar gwamna, tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999.
Can a Kebbi ma, ƙarashen zaɓen zai gudana ne a tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP babbar mai adawa.
Masu kaɗa ƙuri’a 94,209 ake sa rai za su fita a yau don zaɓen da zai raba gardama tsakanin Aminu Mohammed Bande na PDP da kuma Dr. Nasir Idris.
Ɗan takarar jam’iyyar APC dai ya samu ƙuri’a 388,258, yayin da na PDP mai adawa ke da ƙuri’a 342,980 a zaɓen 18 ga watan Maris.
Za a yi zaɓen ne a cikin tashoshin zaɓe 142 da ke faɗin ƙananan hukumomin Kebbi 20.
Zaɓukan ‘yan majalisar dattijai
Cikin mazaɓun ‘yan majalisar dattijai da za a kammala wannan zaɓe na yau Asabar har da mazaɓar Zamfara ta tsakiya, wanda ba kammalu ba tun zaɓen 25 ga watan Fabrairu.
Masu kaɗa ƙuri’a 47, 227 ne za su yi zaɓe a tashoshin zaɓe 83 na ƙananan hukumomin Bunguɗu da Maru da Tsafe.
Fafatawa ta fi zafi ne tsakanin Iƙira Aliyu Bilbis, tsohon ministan yada labarai na Najeriya a jam’iyyar PDP da Sanata Kabiru Garba Marafa na jam’iyyar APC.
Akwai kuma zaɓen ɗan majalisar dattijai na mazaɓar Sokoto ta Gabas, da ke cikin Sokoto, jihar da tashe-tashen hankula suka sanya aka ɗage duk zaɓukan ‘yan majalisun tarayya a ƙarshen watan Fabrairu.
Masu kaɗa ƙuri’a 87, 138 ne ake sa rai za su fita su yi zaɓe a tasoshin zaɓe 169 don tantance mutumin da zai wakilce su a majalisar dattijan Najeriya.
Manyan ‘yan takara a zaɓen akwai Shu’aibu Gwanda Gobir na jam’iyyar PDP wanda ke fafatawa da Ibrahim Lamiɗo na APC
Za a yi zaɓen ne a ƙananan hukumomin Gada da Goronyo da Gwadabawa da Illelah da Isa da Raɓah da Sabon Birni da kuma Wurno
Zaɓen ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Sokoto ta Kudu zai gudana ne a cikin tasoshin zaɓe 156, inda ake sa ran masu kaɗa ƙuri’a 85, 022 za su raba gardama tsakanin ‘yan takarar sanata.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ɗan takara a jam’iyyar PDP, inda yake fuskantar ƙalubale daga Ibrahim Ɗanbaba Dambuwa na APC.
Yabo da Tambuwal da Tureta da Shagari da Keɓɓe da Boɗinga da Denge Shuni su ne ƙananan hukumomin da za a yi zaɓen a Sokoto ta Kudu.
Masu zaɓe 115,266 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri’unsu don fitar da zakaran da zai wakilci mazaɓar ɗan majalisar dattijai ta Sokoto ta Arewa.
Zaɓen dai zai gudana ne a tasoshin kaɗa ƙuri’a 185 da ke faɗin ƙananan hukumomin Wamakko da Tangaza da Binji da Gudu da Kware da Silame da Sokoto ta Arewa da Kudancin Sokoto.
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na APC dai yana fuskantar babban ƙalubale daga mataimakin gwamnan jihar Sokoto Mannir Muhammad Dan’iya na PDP.
Masu zaɓe 13, 243 ne ake sa rai za su fita su kaɗa ƙuri’unsu a mazaɓar ɗan majalisar dattijai ta Kebbi ta Arewa.
Tashoshin zaɓe 23 ne za a yi fafatawar cikinsu a ƙananan hukumomin Augie da Arewa da Bagudo da Argungu da Dandi da kuma Suru.
Zaɓukan ‘yan majalisar wakilai
Sokoto ce kan gaba cikin jihohin da za a ƙarasa zaɓukan ‘yan majalisar wakilai da ba su kammala ba, a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.
Akwai ‘yan majalisar wakilai guda 11 daga jihar da suka haɗar da:
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Rabah-Wurno
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Yabo-Shagari
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Sokoto ta Arewa – Sokoto ta Kudu
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Kware – Wamakko
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Keɓɓe – Tambuwal.
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Isa – Sabon Birni
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gwadabawa – Illelah
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gudu – Tangaza
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gada – Goronyo.
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Bodinga – Denge Shuni – Tureta
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Binji – Silame.
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gusau – Tsafe
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gumi – Bukkuyum
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Arewa – Dandi
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Koko Besse – Maiyama
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Doguwa – Tudun Wada
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Fagge
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Oluyole
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Ibadan ta Arewa maso Gabas – Ibadan Kudu maso Gabas
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Khana Gokana
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Port Harcourt II
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Ikono – Ini
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Abak – Etim Ekpo – Ika
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Takum – Ussa – Donga
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Dekina – Bassa
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Gumel
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Mbaitoli – Ikeduru
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Orhionmwon Uhunwode
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Ezza ta Arewa
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Southern Ijaw
- Mazaɓar ɗan majalisar wakilai ta Ogbaru
Zaɓukan ‘yan majalisar dokokin jiha
Wata sanarwa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta wallafa a shafinta na intanet, ta nuna cewa jihar Kano ce ke da mazaɓun ‘yan majalisar dokokin jiha mafi yawa da za a ƙarasa zaɓen yau Asabar cikinsu.
Ga ƙananan hukumomin da zaɓen zai shafa:
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Takai
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Warawa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Wudil
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ungogo
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gwarzo
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Tudun wada
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gezawa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Makoɗa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gabasawa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Garko
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gaya
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Dawakin Tofa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Danbatta
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ajingi
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Maiyama
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Sakaba
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Jega
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Koko Besse
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Kalgo
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Arewa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Augie
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gwandu
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Kauru
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Giwa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ikara
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Sanga
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Kudan
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Afikpo Southeast
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Afikpo Northwest
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ezza
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ikwo North
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Abakaliki North
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Agwara
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Rafi
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Rijau
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Agaie
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gombi
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Girei
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Toungo
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Numan
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Kankia
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ƙanƙara
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Kurfi
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Dutse
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Birnin Kudu
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta ‘Yan kwashi
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Oredo
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ovia Southwest
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Egor
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Isu
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ahiazu Mbaise
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ideato South
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Etim Ekpo Ika
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ogbia II
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ido Osi I
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Karim Lamido
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Geidam ta Arewa
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Orji River II
- Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ifo