Jihar Kano da kuma Katsina su suka fi kowacce jiha yawan sababbin jami’an yan sanda da aka dauka.
Hukumar yan sandan Najeriya ce ta fitar da jerin sunayen wanda suka samu nasara.
Mutane 37000 ne suka nemi aikin amma mutane 5233 ne suka samu nasara.
Kano na da mutane 308 sai jihar Katsina da take biye mata da mutane 238.
Jihar Oyo itace ta uku da mutane 225 ya yin da birnin tarayya yake da mafi karancin mutane inda birnin ya samu gurbin mutane 44.
Inda aka karkasa mutanen ya zuwa shiya-shiya, shiyar arewa maso yamma ke kan gaba da mutane 1300 sai kuma shiyar kudu maso yamma dake da mutane 921.
Shiyar Arewa ta tsakiya na da mutane 823, kudu maso kudu na da 779, shiyar Arewa maso gabas kuma nada 759.
Shiyar Kudu maso gabas ta samu mutane 651.