Jihohin Najeriya na neman Majalisar wakilai ta sa su cikin harkar samar da wuta.

Asalin hoton, TWITTER/@HOUSENGR

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke kula da harkokin wutar lantarki ya yi zama don jin ra’ayin jama’a, game da wani garambawul da majalisar ke shirin yi ga dokar lantarki domin bai wa jihohi damar shiga harkar samar da wuta.

Kwamitin ya ɗauki matakin ne bayan da jihohi suka nemi a basu damar shiga harkar a matakai daban-daban, da suka haɗa da samarwa da kuma rarrabawa.

Mahukunta a Najeriya dai sun sha nuna rashin gamsuwa da yadda kamfanonin wutar lantarkin suke gudanar da harkokinsu.

Honourable Magaji Ɗa’u Aliyu, shugaban kwamitin ya shaida wa BBC cewa “akwai kamfanin da ke ruwa da tsaki wajen tafiyar da harkokin wutar lantarki a ƙasar, sai dai ya ce jihohi a yanzu sun nemi a basu dama “su je su yi nasu”.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like