
Asalin hoton, Getty Images
Cutar kansa da tauraron dan wasan ƙwallon ƙafa na duniya Pele ke fama da ita ta kara tsanani, a cewar likitocin asibitin São Paulo inda yake jinya.
Mai shekaru 82 da ya lashe Kofin Duniya har sau uku da Brazil, ya shafe makonni uku a asibitin yana jinya.
‘Yarsa Kelly Nascimento ta rubuta a shafin Instagram cewa a asibiti mahaifin nata zai yi Kirsimeti.
Sanarwar asibitin Israelita Albert Einstein ta ce Pele ‘’na bukatar kulawa ta musamman da ke da alaka da cutar koda da zuciya da ke damunsa, kuma cutukan sun tashi ne saboda cutar kansar da ke jikinsa ta yi tsanani.’’
Ko a watan Satumban 2021 an yi wa Pele tiyata a hanjinsa, kuma tun lokacin ya ke jinya akai-akai.
Yan wasan Brazil sun yi jaje ga Pele, bayan nasarar da suka yi a wasansu da Koriya ta Kudu a gasar Qatar 2022, inda suka rika daga hotonsa.
Likitoci a asibitin na Sao Paulo sun ce jikinsa na karbar magani a halin da ake ciki.
Pele ne dan wasan da yafi ci wa Brazil kwallo a tarihi, inda ya ci kwallaye 77 a wasanni 92.
Ya kuma taimaka wa kasarsa ta lashe kofin duniya a shekarun 1958 da 1962, da kuma 1970.