Jinkirin ci gaba da shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisan kai ba da gangan ba ne – Gwamnatin Kano



Ado Doguwa

Asalin hoton, INEC/ TWITTER

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan zargin da wasu ‘yan fafutuka ke yi cewa ta ƙi gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai a gaban kotu.

‘Yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a ƙarshen watan Fabarairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zargin ya harbi wasu mutane, kwana ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudun wada.

Sun kuma tuhumi ɗan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas a ƙaramar hukumar Doguwa lokacin da ake karɓar sakamakon zaɓe.

Kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like