Jiragen yakin sama na Sojan Nijeriya sun kai jerin hare hare a wani sabon sansanin mayakan Boko Haram wanda aka gano a Kudancin Tumbum Rogo da ke Arewacin jihar Borno.
Kakakin Sojan Sama, Group Kyaftin Ayodele Famuyiwa ya ce sakamakon wani bincike ya nuna cewa mayakan Boko Haram da suka kaiwa sojoji hari a Kangarwa a ranar 12 ga wannan wata, sun boye ne a wannan sansanin.