Rahotanni daga jihar Borno na cewa, mutane da dama ne ake fargabar sun rasa rayukansu bayan da jiragen yakin sojin Nijeriya suka jefa bama-bamai bisa kuskure kan fararen hula a kauyen Rann inda akwai sansanin ‘yan gudun hijra a jihar Borno.
A cewar Rundunar sojin cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wanda ya faru a karamar hukumar Kale-balge, sun hada da jami’an lafiya na MSF da kungiyar agaji ta Red Cross.
Shugaban rundudar yaki da Boko Haram Manjo Janar Lucky Irabor ya bayyanawa manema labarai cewa an samu mutuwa da raunuka, har da sojoji a cikin wadanda suka jikkata. a harin.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta Nijeriya Janar Rabe Abubakar ya ce, sun kadu kan wannan kuskure da ya faru.
Rabe Abubakar, ya kara da cewa, lamarin ya faru ne bayan sun samu labarin cewa mayakan Boko Haram sun taru a wani waje da shirin kai hari.
”Amma a bisa tsautsayi sai ya fada wannan kauye. Ba da niyya mu kai hakan ba, kuma hakan dama kan faru a yankunan da ake yaki,” in ji Janar Rabe.