Har yanzu shugaban kasa,Muhammad Buhari ya gaza sauka a birnin Abuja kwana biyu bayan da jirginsa ya baro kasar Amurka.
Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasar ya ce shugaban kasar ya tsaya a birnin London sakamakon yar matsala da jirginsa ya samu kuma zai dawo gida nan ba da dadewa ba.
Ana sa ran isowar shugaban birnin Abuja a ranar Laraba kana daga bisani, a ranar Juma’a ya wuce garin Daura mahaifarsa inda zai huta na yan kwanaki.
Tuni dai tawagar shugaban da za su tarbe shi sun isa garin na Daura.
Sai dai bayan wannan tsaiko da aka samu sun kama hanyarsu ta komawa Abuja.
Jirgin shugaban kasar ya bar filin saman soji dake birnin Washington da safiyar ranar Talata.