Jirgin kasa dauke da kaya yayi hatsari a Ibadan


Wani jirgin kasa na daukar kaya yayi hatsari inda ya makale a mahadar layin dogo ta  Omi- Adio dake kan titin Abeokuta zuwa Ibadan, inda hakan ya jawo cinkoson ababen hawa.

 Jirgin kasar dake da namba 90035 yana dauke da kontena guda ashirin ta kamfanin Dangote ya fadi ne a wurin da gadar jirgin ta tsallaka titin na Abeokuta zuwa Ibadan, inda ya hana motoci ta kowanne bangare damar tsallakawa.

Direban jirgin ya fice daga jirgin inda ya nufi tashar jirgin kasa dake  Ibadan, wacce ba tafi tafiyar minti 20 ba a mota.

Motoci a kowanne bangare sun juya domin lalubo wata hanyar da za ta kai su wuraren da suka nufa.

You may also like