Wani jirgin kasan da ya taso daga Kano zuwa Lagos ya yi karo da wata tirela a matsallakar layin dogo ta Kawon Kaduna a daren ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda hukumar kiyaye hadurra ta FRSC ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na NAN.
Shugaban FRSC na jihar, Mista Francis Udoma, ya ce al’amarin wanda ya haddasa mummunan cunkoso har zuwa safiyar jiya ya faru da misalin karfe uku na daren Talata amma babu asarar rai ko daya. Udoma ya ce jirgin yana dauke da fasinjoji ciki har da sojoji yayin da ya daki wata tirelar rake inda ta rabe gida biyu.
Hukumar ta FRSC wacce ta zargi cewar direban tirelar kurma kurma ne ta ce tun daga nesa matukin jirgin kasar yake masa hon da fitila amma sai da ya tsallako.