Jirgin Kasar Kaduna zuwa Abuja ya tara miliyan biyar(5)  a sati biyu.  


Shugaban Tafiyar da harkar sufuri na jirgin kasa a Nigeria Mr Fidet Ikhiria Nigerian Railway Corporation (NRC), yace jirgin kasar da ya fara daukar Fasinjoji daga kaduna zuwa abuja sati biyu da suka gabata ya tara kudi har miliyan biyar a sati biyun.

Shugaban ya kara da cewa jirgin mai daukar mutane 320, yana iya daukan mutane 1000 a duk rana domin sufuri zuwa Abuja daga kaduna.

A satin farko da fara sufurin an samu kudi har miliyan biyu da dubu dari biyu (2.2millions), a sati na biyu kuma an samu miliyan biyu da dubu Dari tara (2.9millions) wanda hakan ba karamin ci gaba bane ga kasar najeriya.

Mr Ikhiria ya kara da cewa wu kansu ma’aikatan suna mamaki da yawan mutanen da suke zuwa domin hawa jirgin zuwa abuja aga kaduna ko kuma kaduna daga abuja.

Daga karshe yace,  suna iya bakin kokarinsu wajen

Tabbatar da cikakken tsaro ga Fasinjoji.

You may also like