Jirgi mai saukar ungulu da ya kai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wajen bikin yaye manyan jami’an kwastam a kwalejin horar da manyan jami’an kwastam dake Gwagwalada a Abuja a jiya ya yi saukar gaggawa jim kadan bayan tashinsa.
Mataimakin shugaban kasar na kan hanyarsa ta komawa fadar Aso Rock bayan taron lokacin da jirgin da yake ciki mai saukar ungulu ya samu matsala.
An gano jirgin yana fitar da wani hayaki dai-dai lokacin da yake kokarin saukar gaggawa bayan da ya tashi.
Mataimakin shugaban ya koma fadar cikin mota.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana cewa mai gidansa ya gujewa yin amfani da jirgin dalilin wata yar matsala.