Jirgin saman Isra’ila da ke kai wa Falasdinawa hari ya fado


 

Wani jirgin saman F-16 da Isra’ila ta kai hari zirin Gaza da shi ya fado a sansanin Ramon tare da kamawa da wuta inda matukin jirgin Kaftin Ohad Cohen Nov ya mutu.

Mataimakin matukin jirgin kuma ya samu rauni kadan.

Ba a bayar da wasu dalilai da suka janyo konewar jirgin ba inda rundunar sojin saman ─▒sra’ila ta fara gudanar da bincike.

Tashar Talabijin ta Channel 10 da ke Isra’ila ta bayar da labarin cewa, jirgin ya samu matsala ne inda kuma ya kama da wuta nan take.

A ranar Larabar nan Isra’ila ta kai hare-haren bam sau 35 a garin Sderot na Gaza bisa zargin cewa, an harba makamin roka zwa Isra’ila daga garin.

You may also like