Jirgin saman kamfanin Dana ya kauce daga kan hanyarsa ya shiga  cikin daji a filin jirgin saman Fatakwal


Wani jirgin saman kamfanin Dana da ya tashi daga Abuja zuwa birnin Fatakwal ya gaza ɗaya akan titinsa inda ya shiga ciki daji.

An rawaito cewa jirgin ya taso ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja amma mai makon ya tsaya a inda yakamata dake titin jirgin sai ya ci birki a cikin daji.

An kwashe dukkanin fasinjojin dake cikin jirgin daga dajin.

Hukumar dake kula da filayen jiragen sama ta ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace babu wanda ya jikkata.

Lamarin da ake zargin mamakon ruwan sama da kuma iska me ƙarfi ce suka haddasa kaucewar jirgin daga kan titin nasa.

You may also like