Jirgin Saman Soja Ya Fado A Kaduna Wani jirgin sama mallakar rundunar  sojin saman Najeriya ya fado a Kaduna.

Olatokunbo Adesanya daraktan yada labarai da hulda da jama’a  na rundunar ya sanar da haka a wata sanarwa da yafitar yau Alhamis, yace jirgin yayi hatsari ne lokacin da yake wani aiki a jihar.

Yace daya daga cikin mai koyar da tukin jirgi a rundunar ya rasa ransa a hatsarin.

Ya kuma ce har ya zuwa yanzu ba a san musabbabin faduwar jirgin ba sai dai yace babban hafsan sojin saman Najeriya ya kaddamar da bincike don gano dalilin faduwar jirgin.

” wani jirgin sama na sojin saman Najeriya mai suna Air Beetle,ya fadi a Kaduna lokacin da yake wani aiki, mutum guda daya dake cikin jirgin wanda yana daya daga cikin kwararrun masu koyar da tuki a rundunar ya rasa ransa a hatsarin,” Adesanya yace.

 “Ba a san dalilin faruwar hatsarin ba, amma babban hafsan sojin sama ya bada umarnin kafa kwamitin bincike da zai gano dalilin faruwar hatsarin, hatsarin da yafaru wata tunatarwa ce kan  irin kalubalen  dake tattare da tukin jirgin sama. Babban hafsan sojin sama da kuma dukkanin sojin saman Najeriya suna mika sakon alhininsu ga iyalan marigayi mai koyar da tukin jirgin.”

You may also like