Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da faduwar jirginta na yaki a tekun Meditarinia
A wata sanarwa da Ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar a marecen jiya Litinin ta tabbatar da faduwar jirgin yakinta samfarin Mik 29 da ya kasance kalkashin ma’aikatar tsaron saman kasar.
Shidai wannan jirgi na daga cikin jerin jiragen yakin kasar Rasha dake jibke a babban jirgin ruwan daukan jiragen saman kasar dake cikin tekum Meditrenia, kuma dukkanin matukan jirgin yakin da ya fadi sun kubuta, tuni jami’an Agajin kasar dake cikin tekun suka isa da su zuwa sansaninsu dake cikin tekun.
An bayyana dalilin faduwar wannan jirgi da matsalar na’ura,tun a ranar 11 ga wannan Wata na Nuwamba da muke ciki ne jiragen yakin na kasar Rasha dake tekum meditrenia suka fara sintiri domin gano maboyar ‘yan ta’addar Siriya a cikin kasar.