Jirwaye Mai Kamar Wanka: Tsokaci Akan Hatsarin Da Yusuf Buhari YaYi


Tsakani da Allah idan aka ce mun dangidan Atiku, Kwankwaso ko Jonathan ne ya hau babur din tsere na miliyoyin kudi, ya je tsere cikin y’ay’an ma su dukiya da alfarma, ko damuwa ba Zan yi ba balle in waiwaya.

Amma ace Dan Buhari na cikin shi, Buharinnan da yake tilasta mana koyan tsantseni, muna fama da kudin man fetur bayan mun saba da zagwanyewar albashi sakamakon tsadar Kaya, wannan abun bakin ciki ne.

Ni talaka ne kuma dan talakawa, irin wannan labarin yana karya Mana gwiwar marawa Buhari baya. Saboda haka; ya zama dole a dauki mataki na gaskiya, kuma Kar asake Jin irin wannan labari.

Muna tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ko ba dan komai ba, Shugaban mu ne, dole in muna neman zaman lafiya sai mun marawa shugaba baya kuma munyi masa biyayya

You may also like