Jita-Jitar Wasanni: Bonucci Ya Amince Zai Koma AC MilanMai tsaron Bayan Kungiyar Juventus, Leonardo Bonucci ya amince zai koma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan akan kudi £7 million. 

Barcelona sun Daina Neman Dan wasan Bayan Arsenal Bellarin. 

Tottenham sun gargadi Manchester united da su daina taya musu dan wasa Dier Dan Bana siyarwa bane. 

Westbrom Albion Suna neman Smalling da Phil Jones, wadanda dukkansu ‘Yan bayan Manchester United ne. 

Arsene Wenger ya tattauna da kylian Mbappe Akan ya koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kakar wasanni mai zuwa. 

Chelsea Na neman dan wasan gaban Sevilla, Vitolo. 

You may also like