Johnathan Ya Nesanta Kansa Da Modu Sheriff 



Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya musanta jita jitar cewa ya amince da tsohon Gwamnan Borno, Modu Sheriff a matsayin Shugaban jam’iyyar PDP na kasa a bayan wata ziyara da ya kai masa.
Kakakin Tsohon Shugaban, Mista Eze ya ce Jonathan ya karbi bakuncin Modu Sheriff ne a matsayinsa na Shugaban jam’iyyar kuma a yunkurin ganin an samu maslaha a rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam’iyyar.

You may also like