Jonathan yasa kasar mu cikin yunwa da kunci – Pastor Mbaka


ubaka

Pastor Mbaka yace Jonathan da jam’iyar PDP ne suka saka kasar nan tamu  a yanayin kuncin da yunwa, yace mutane suna zargin Buhari bayan ga wayanda suka lalata tattalin arzikin kasar nan a bayane ya kara dace wa, sun jawon hankalin shugaban kasa akan yasan yanayin da kasar take ciki na yunwa da kunci kuma a san mafita akan al’amarin.

Paston ya kara da cewa duk da shekarun da Jonathan yayi akan mulki ba abinda yayi wa Niger Delta,wanna abin kunya ne  ace i’in da matatar mai yake an barshi ba gyara ko kadan,babu wata cigaba da yasamar musu,yace abinda yafi ciwo shine yanda mutanan mu ke saurin dora wa wani laifin wani.

You may also like