A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaban Majalisar Dattawa Senata Bukola Saraki ya Jajantawa illahirin iyalan shugaba Buhari akan hatsarin da dan su Yusuf ya yi, sannan ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya
Shima tsohon shugaba kasa Goodluck Jonathan Cewa yayi “Ina kasar Laberiya don aikin sanya ido akan babban zaben kasar, kwatsam sai naji mummunan labari. A madadin ni da iyalai na muna addu’ar Allah ya bawa Yusu Buhari lafiya.
Kawo yanzu rahotanni na cewar da yiwuwar a shilla da Yusuf kasar Jamus domin cigaba da jinya.