Jonathan ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Anambra


Tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan a jiya yace hanya daya da ƙabilar Igbo za su bi su kawo karshen wariyar da ake nuna musu shine su kawar da Jam’iyar APC da kuma APGA daga kan mulki ta hanyar kin kada musu kuri’a farawa daga zaben gwamnan Anambra.

Ya shawarci mutanen jihar da su dawo da jam’iyar PDP kan mulki ta hanyar zaben  dan takararta,Mista Oseleka Obaze.

 Jonathan wanda ya jagoranci gwamnonin jahohin, Rivers, Delta, Taraba, Gombe, Ebonyi, Ekiti da  mataimakin gwamnan Akwa Ibom da kuma tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel, zuwa wajen gangamin rufe yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar karkashin jami’iyar ta PDP.
Anasa jawabin tsohon gwamnan jihar, Peter Obi, ya bayyana kasancewar Obiano gwamna  a matsayin kuskure da yakamata mutanen jihar su gyara.

A jawabinsu daban-daban gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da kuma na Ekiti Ayo Fayose sun shawarci mutane da su zaɓi dan takarar jam’iyar PDP domin kawo karshen wahalhalun da suke ciki.

You may also like