Jonathan ya yi ganawar sirri da Babangida a Minna


Tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan yayi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa dake Minna.

An rawaito cewa Jonathan ya isa gidan cikin wata motar silke kirar GMC mai dauke da lamba ABJ 961ER cikin jerin gwanon motoci 8 dake cikin a yarinsa,sun kuma isa gidan da karfe 10 na safe.

Tattaunawar tsakanin shugabannin biyu da suka fara mintuna kadan bayan karfe goma basu kammala ba  sai karfe 12:14 na rana.

Jonathan yaki yarda ya bayyana dalilin ziyararsa inda yace ziyara ce ta kashin kai.

Da yan jarida suka matsa shi da tambaya sai yace yazo ne  domin duba  tsohon shugaban bayan dawowa da yayi daga kasashen waje inda aka duba lafiyarsa.

” Banga Janaral Babangida ba tun lokacin da ya dawo daga jinya saboda haka naga cewa yanzu ne lokacin da ya dace nayi hakan,” Jonathan ya ce.

Da aka nemi ya yi tsokaci kan yanayin siyasa da kuma tattalin arziki kasarnan tsohon shugaban ya ce shi ne yanzu yayi ritaya daga siyasa 

You may also like