
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta amince da yarjejeniyar daukar dan kwallon Italiya da ke murza leda a Chelsea Jorginho.
Dan kwallon mai shekaru 31, ya koma Chelsea ne daga Napoli a shekara ta 2014 kuma saura wata shida kwantaraginsa ta kare a Stamford Bridge.
Arsenal ta mayar da hankali ne a kan Jorginho bayan Brighton ta ki sallama ma ta Caicedo.
Kungiyar Brighton ta ce Caicedo ba na sayar wa bane, kuma akwai alamun cewa dan kwallon Ecuador din ba zai bar Brighton.
Jorginho zai kasance dan wasa na uku da Arsenal ta saya a watan Janairu bayan dan kwallon Poland Jakub Kiwior daga Spezia a kan Euro miliyan 20 sai kuma dan kwallon Belgium Leandro Trossard wanda ta dauko daga Brighton.
Jorginho ya ci kwallo 29 a cikin wasa 213 da ya buga wa Chelsea kuma ya lashe gasar Champions da Europa da Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup.