Joseph Yobo ya zama Jakadan FIFA


joseph-yobo

 

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) Mista Gianni Infantino ya nada  tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles a matsayin Jakada.

Shugaban ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kawo Najeriya ta kwana biyu a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi.
Wannan matsayi da FIFA ta ba Yobo alhakinsa ya kula da yadda za a bunkasa gasar rukunin firimiya ta Najeriya don ganin martabar Najeriya ta daukaka a idon duniya.  Sannan alhakinsa ne ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya janyo hankalin masu zuba jari a harkar kwallon kafa sun shigo Najeriya don bayar da tasu gudunmuwar.
A sakon da ya aika ta kafar sadarwar zumuntarsa ta Tweeter, Yobo ya ce ya ji dadi da wannan karramci na zabarsa Jakadan kwallon kafa na Najeriya da Hukumar FIFA ta yi, inda ya sha alwashin ganin ya yi duk mai yiwuwa wajen daukaka martabar kwallon kafa a Najeriya.
“Yakamata mu inganta gasar firimiya ta Najeriya, don ta wannan hanya ce kadai za mu samu matsayin da ya dace da mu a fagen kwallon kafa a duniya.”
Daga nan dan kwallon ya yaba wa wadansu daga cikin jami’an hukumar kwallon kafa ta NFF, Shehu Dikko da Nduka Irabor a kokarin da suke yi na ganin sun farfado da martabar gasar rukunin firimiya ta Najeriya.
Yobo ya kuduri aniyar yin aiki tare da su, don ganin an cimma burin da aka sanya a gaba na farfado da martabar kwallon kafa a Najeriya.

You may also like