Kada Ku Yimin Fatan Mutuwa, Har Yanzu Kuna Bukata Ta, Obasanjo Ya Fadawa Matasa


Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci matasa da kada suyi masa fatan mutuwa shi da sauran manyan dattijai masu fada aji a kasarnan.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a jiya Lahadi,  a wurin taron matasa da cibiyar cigaban matasa ta dakin karatu na Olusegun Obasanjo ta shirya a Abeokuta babban birnin jihar Ogun. 

Obasanjo ya shawarci matasa da kada su fidda tsammani kana su kara hakuri. 

” kada kuyi mana fatan mutuwa,kada kuyi mana fatan mu bace saboda zaku bukace,kuna bukatar mu domin shiryaku wajen tunkarar abinda zai faru a gaba,kuna bukatar kwarewarmu da kuma taimakon wasu daga cikin mu,” yace.

 ” kada ku fidda tsammani,kada gwiwowinku suyi sanyi. Duk sanda naje kasar waje, suna yawan tambaya ta me nake tsoro game da nahiyar Afirika da kuma Najeriya, Ina fada musu babban abin da nafi tsoro shine fushin matasa da kuma yawa da matasa ke kara yi wanda bashi da iyaka. 

” muna da Boko Haram a Arewa, MASSOB da IPOB a yankin Kudu maso gabas da kuma OPC a yankin kudu maso yamma ga kuma tsagerun yankin Neja Dalta duk kaninsu suna bayyana fushi da kuma yadda suke ganin an tauye musu hakki. “

You may also like