Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suka tayar da hankalin su dangane da yanayin rashin lafiyar sa da su kwantar da hankalin su kada wani abu ya daga musu hankali.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, Buhari ya godewa miliyoyin ‘yan Najeriya akan Addu’o’in samun Lafiya da suke yi masa a Masallatai da Cocina.