Kimanin Mutane 40 Ne Suka Rasa Ransu A Garin Godogodo Dake Kudancin Jihar Kaduna A Rikici Tsakanin Makiyaya Da Mazauna Garin
Rikicin wanda aka soma shi tun ranar Asabar din da ta gabata, duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a yankin, amma mazauna garin sun koka da yadda gwamnatin tarayya da ta jiha ta ki kawo musu daukin gaggawa.