Gwamnatin kasar Ethiopiya ta kafa dokar ta baci ta tsawon watannin shida a duk fadin kasar, biyo bayan tashin hankalin da aka yi a makon jiya.

An dai dau wannan doka ce bayan taron majalisar minitocin na jami’an gamnatin inda aka tafka muhawar mai surfi a game da asarar rayuka da kadarori da aka samu a sakamakon zanga-zangar da a ka yi. A ranar biyu ga watan Oktoba wani bikin al’adu na addini da aka yi a garin Oromo da ke a yankin tsakiyya na kasar ya rikide ya koma zanga zangar kyamar gwamnatin wanda a ciki mutane 55 suka mutu.Sama da shekaru 25 ke nan da ‘yan kabilar Oromo da Amhara na Ethiopiya wadanda sune ke da rinjaye a kasar ke jagorantar boran adawa da gwamnatin saboda abin da suka kira wariya da ake nuna musu.