Kafafan Yada Labarai Ne Ke Zuzuta Wahala a Nijeriya – NAN


Shugaban kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya koka da yadda wasu mutane ke kara zuzuta wahala da yunwa da ake fuskanta a Nijeriya a lokacin mulkin Buhari.

Wannan batu ya bayyana ne a shafinsa na Facebook inda ya zargi wasu kafofin yada labaran Nijeriya da yin mummnan frofaganda domin muzanta gwamnatin Muhammadu Buhari.

Bayo wanda fitaccen dan jarida ne ya bayyana cewa binciken da ya gudanar a jahohin Bauchi da Jos sun nuna masa cewa har yanzu kayan abinci suna araha, ba kamar yadda ake ta yadawa ba.

Ya ce banda kafafen yada labarai, akwai kuma batun ‘yan adawa wadanda suka fadi a zaben bara, suma suna da hannu wajen kara gishiri a batun wahalar da ake sha.

Bayo Onanuga ya ce, duk da cewa, akwai tashin farashin kaya, amma shi ya yi imanin ana zuguguta lamarin da nufin bata sunan gwamnatin Buhari.

Babu mamaki kuwa wannan magana ta Bayo ta tsokano inda yakewa mutane kaikayi, inda ta haifar da cece kuce a shafukan zumunta.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like