
Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta ci Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen quarter finals a Champions League da suka kara ranar Talata a Etihad.
Minti 27 da fara wasa City ta ci kwallon ta hannun Rodrigo Hernandez, bayan da suka koma zagaye na biyu Bernardo Silva ya kara na biyu, Erling Haaland ya ci na uku minti bakwai tsakani.
Kwallo na 45 da Haaland ya ci a bana a dukkan fafatawa, ba wani dan wasan dake buga Premier mai wannan bajintar.
Wasa na bakwai da suka kara a Champions League a tsakaninsu, City ta ci hudu, Bayern ta yi nasara a uku.
City ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da RB Leipzig, ita kuwa Bayern ita ce ta yi waje da Paris St Germain.
Wannan shine karon farko da suka kara a quarter finals, bayan da sauran fafatawar da suka yi a cikin rukuni suka yi.
Wannan shine karo na 21 da Bayern ta kai quarter finals a Champions League, wadda ta dara Real Madrid mai 19.
Manchester City ce kadai cikin masu kai wa zagayen daf da na kusa da na karshe a kaka shida a jere a baya.
Wasa na karshe tsakanin City da Bayern shine na 2014, wanda kungiyar Ingila ta yi nasara a gida da cin 3-2.
Kowacce ta ci uku-uku, wannan shine wasan farko da za su kece raini a zagayen quarter finals, a cikin rukuni suka kara a baya a fafatawa shida.
Wasa shida tsakanin Man City da Bayern Munich
Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2014
Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2014
Champions League Tu 10Dec 2013
Champions League We 02Oct 2013
Champions League We 07Dec 2011
Champions League Tu 27Sep 2011
Bayern ta kai zagayen gaba a wasa biyar daga shida da ta fuskanci kungiyoyin Ingila a ziri kwalle, in banda kakar 2018/19 a zagaye na biyu da Liverpool.
Bayern ta ci wasa hudu a jere a kan kungiyoyin Premier League, wasan farko da aka doke ta a karawa biyar da ta kai ziyara Ingila, wadda ta ci uku da canjaras daya.
Sai dai City ta ci wasa na 11 a jere a gida a kan kungiyoyin Jamus a Champions League da cin kwallo 42 -10.
Ranar Laraba 19 ga watan Afirilu, Bayern Munich za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu a Champions League zagayen quarter finals.