Kafewar Madatsar Ruwa, Ya Janyo Manoman Rani Sun Tafka Asara, A Jihar Katsina 


Daruruwan manoman rani da suke amfani da madatsar ta Musawa a jihar Katsina, na can na kirga irin asarar da sukayi bayan da ruwan dake madatsar ya kare. 

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa, shukokin manoman na matakin girma daban-daban, inda suka fara bushewa, hakan yasa wasu manoman fara debe amfanin gonarsu tun kafin ya nuna, domin rage asara. 

Shugaban manoman rani na yankin Alhaji Idris Abdullahi, ya fadawa NAN cewa sama da manoma 150 wannan abun ya shafa. 

Abdullahi yayi kiyasin manoman, sunyi asarar kudi kimanin naira miliyan 30.

Yace kimanin hekta 150 ta tumatir,masara,albasa,alkama da sauran kayayyaki suka lalace.

Abdullahi ya shawarci gwamnati da ta yashe madatsar ruwan kafin ruwan damuna ya sauka, kana ta bawa manoman tallafi don rage radadin asarar da sukayi. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like