Kagame ya karɓi ragamar  jagorancin ƙungiyar AU


Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame, a yau ya karbi ragamar jagorancin Ƙungiyar Tarayyar Afirka AU.

Kagame ya karɓi jagorancin ƙungiyar daga shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Theodora Obiang Nguema Mbasogo.

A jawabinsa na karɓar shugabanci, Kagame ya jaddada bukatar samar da wata hanya da zata samar da yalwar arziki ga ƴan Afirka, musamman matasa.

 Sabon shugaban kungiyar ta AU, wanda ya lura cewa ƴan Afirika sun cancanci samun rayuwa mai kyau anan gaba, yace haɗin kai shine ya zama dole  abinda Shugabannin ƙasashen yankin zasu mai da hankali anan gaba.

 Ya ce matasan Afrika, da kuma ƙwararru na da rawar daza su taka inda ya ƙara ƙarfafa cewa dole ne a bawa mata matsayinsu.

Ya kuma godewa Shugabannin nahiyar kan ƙwarin gwiwar da suke dashi akansa na ya jagorance su inda yace zai yi iya ƙoƙarinsa.

You may also like