Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan Kwalekwalen ‘yan gudun hijra a gabar tekun Libiya
Kamfanin dillancin Labaran France Press ta nakalto wani jami’in kasar Libiya da ya bukaci a sakeye sunansa na cewa harin da aka kai kan kwalekwalen bakin hauren dake kokarin zuwa kasashen Turai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4 tare kuma bacewar wasu 11 na daban.
Ya zuwa yanzu dai babu wani mutum ko kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, a ranar Talatar da ta gabata ma an gano birbidin wani kwalekwalen dake dauke da bakin haure a gaban tekun na Libiya, lamarin da yayi sanadiyar hallakar mutane 28.
Har ila yau a ranar Litinin din da ta gabata sama da bakin haure dubu 6 ne aka ceto daga hadarin hallaka mafi yawan su ‘yan kasashen Afirka bayan da wasu 9 na daban sun hallaka a gabar tekun na Libiya.
Kasashen Turai dai na fuskantar kwararen bakin haure daga kasashen da ake yaki na gabas ta tsakiya da kuma Afirka, a shekarar 2015 din da ta gabata sama da Mutane milyan daya da dubu dari ne suka yi hijra zuwa kasashen Turai.