An kai hari a makarantar koyar da addini


 

 

An kai wani hari a makarantar koyar da addini na Mina Hindholm a garin Fuglebjerg da ke kusa da birnin Copehang na kasar Denmark.

Shugaban makarantar sakandaren Hindholm Ahmet İhsan Deniz ya sanarda cewa, wannan shi ne karo na hudu da wasu makiya addini suka kaiwa makarantar hari.

Deniz ya kara da cewa, jiya dare ne wasu suka kai hari a makarantar a dai-dai wurin da suke da tabbacin cewa babu kamera amma sai dai an kaiwa ‘yan sanda kara.

Bayan kafafan yada labarai sun sawa makaraktar suna da “sakantadaren musulmai” ne sai aka fara kaiwa makarantar hare-hare.

Deniz ya kuma kara da cewa, a cikin ‘yan kwanakin nan ma’aikatan ministan ilimin kasar Denmark sun ziyarci kasar inda suka bayyana farin cikinsu game da makarantar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like