An Kai Hari A Masallacin ‘Yan Shi’a A Kabul


 

Rahotanni daga Afganistan na cewa a kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu kana wasu masu yawa suka raunana a yayin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da boma boman da yayi jigida dasu a masallacin ‘yan shi’a na Baqirul Olum dake yammacin kasar Kabul babban birnin Kasar.

Wannan harin dai na zuwa ne a yayin da duniyar shi’a ke gudanar da tarurukan arba’in na juyayin shahadar jikan mazon Allah Imam Hussain (AS).

Daya daga cikin wadanda suka ji rauni a harin ya shaidawa kanfanin dilancin labaren Faransa na AFP cewa, yana cikin Sallah kwasam sai ya ji kara fashewar wani abu mai karfin gaske, kuma nan take ya gane ma iddanunsa gababauwan jikin mutane da jini ko ina.

Har kawo lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai sau tarin yawa akan nuna ‘yar yatsa ga kungiyar ‘yan ta’addan nan ta (IS).

A nata bangare kungiyar ‘yan taliban dake fada da makamai nisanta kan ta tayi da kai wannan harin.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka kaiwa ‘yan shi’a hari a wannan kasa ta Afganistan inda a ko a yayin tarurukan Ashura a ranar 13 ga watan Oktoba kungiyar IS ta dau alhakin  kai wasu jerin hare hare da sukayi sanadin mutuwar mutane 30 tare da jikkata wasu kimanin 100 a Kabul, Mazar-i-Sharif babban birnin arewacin kasar.

You may also like