An kai hari ofishin yakin neman zaben Trump a Amurka


 

An kai hari ofishin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republicans Donald Trump.

Wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a ofishin da ke Arewacin Carolina inda suka cinna wuta a cikinsa.

A jikin bangon ofishin wanda ya samu matsala an rubuta “‘Yan Republicans masu akidar Nazi su bar wannan gari ko kuma..”

Babu wani da ya samu rauni sakamakon harin amma kuma an lalata ginin ofishin.

Dan takarar jam’iyyar republicans Donald Trump ya ce, sakamakon ganin suna kan gaba a zaben kasar ne ya sanya magoya bayan Hillary Clinton da jam’iyyar Democrats suka kai hari a ofishinsu.

A sanarwar da Clinton ta fitar a shafin sada zumunta na yanar gizo kuma ta bayyana cewa, ba za a amince da irin wannan halayya ba.

You may also like