An kai hari a wata kasuwa a india


Gidan talabijin na gwamnatin India ya ce akalla mutum goma sha uku sun mutu yayin da ashirin suka samu rauni a wani hari da aka kai a kan wata kasuwa a jihar Assam dake arewa maso gabashin kasar.

‘Yan sanda sun dora alhakin harin a kan wata kungiyar masu tayar da kayar baya da ake kira National Democratic Front of Bodoland — sun kuma ce sun kashe dan bindiga daya.

Jami’an tsaro sun killace yankin da tashin hankali ya faru a garin Kokrajhar. Suna kuma neman sauran maharan.

Mayakn sa-kai na kabilar Bodo suna neman a bai wa yankin Bodoland matsayin jiha. Tun shekara ta 2012 yankin ke fama da rikice-rikicen kabilanci.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like