An kai harin bam a Jamus


jamuss

A Jamus mutane 12 sun ji rauni a daren jiya Lahadi a cikin wani harin kunar bakin wake da wani matashi dan Siriya ya kai a birnin Ansbach na kusa da birnin Nuremberg.

Ministan cikin gidan jihar Bavariya Joachim Herrmann ya shaida wa manema labarai cewa dan kunar bakin waken wanda ya rasu a harin ya tayar da bam din da ke jikinsa ne da misalin karfe takwas da mintin 12 na daran jiya a bakin kofar wani wuri da ake gudanar da bikin al’adun a birnin na Ansbach na kusa da birnin Nuremberg bayan da jami’an tsaro suka hana shi kutsawa cikin taron.

Ministan ya kara da cewa matashi dan shekaru 27 dan asalin kasar Siriya ya shigo Jamus shekaru biyu da suka gabata inda a bara ya nemi takardan izinin zama a kasar amma aka hana shi. Rahotanni sun nuna cewar a baya sau biyu ya yi yinkurin kashe kansa kafin ya hallaka kansa a cikin wani harin na kunar bakin wake da ya kai.

Wannan dai shi ne hari na hudu da kasar Jamus ta fuskanta a cikin mako daya inda a ranar Juma’ar da ta gabata wani dan bindiga ya halaka mutane tara a wata cibiyar kasuwancin birnin Munich. Dama dai a safiyar jiya Lahadin wani dan gudun hijirar Siriya dan shekaru 21 dauke da adda ya halaka wata mata a birnin Reutlingen na Kudancin kasar. A ranar Litinin da ta gabata kuwa wani matashi ya kai hari da gatari kan fasinjan wani jirgin kasa inda ya jikkata mutane hudu kafin ‘yan sanda su bindige shi.

You may also like