An kai harin bam a Somaliya


 

 

An kai harin bam a wani kasuwa a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya inda aka kashe mutane akalla 10 tare da jikkata wasu da dama.

A halin yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

An kai harin ne bayan dakarun gamayyar Afirka da na Somaliya suka sanarda cewa suna shirin kaiwa ‘yan ta’addan Ashabab hari.

Makonni ukun da suka gabata, ‘yan ta’addan Ashabab reshe na Al-Qaeda sun kai ‘yan sanda harin bam inda aka kashe mutane 9.

A cikin ‘yan shekaru 10 Ashabab ta kai hare-hare da dama tare da kwace kauyuka da dama.

You may also like