An kai harin bindiga a gidan rawa da ke Florida


Jami’an ‘yan sandan Amurka sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma raunana 16 a harin bindigar da aka kai wani gidan rawa da ke birnin Fort Myers na jihar Florida.

An kaddamar da harin ne da misalin karfe 12:30 na daren da ya gabata kuma a daidai lokacin da gungun matasa ke taron shagali a gidan rawar na Club Blu.

Sanarwar da jami’an ‘yan sandan suka fitar ta ce, wadanda suka samu raunukan na kwance a asibiti kuma wasu daga cikin su na fuskantar barazanar rasa rayukansu.

Jami’an ‘yan sandan na kokarin gano makasudin kaddamar da harin duk da cewa an kama mutane uku sakamakon aukuwar lamarin.

Sabon harin na zuwa ne bayan makwanni shida da wani matashi mai suna Omar Mateen ya hallaka mutane 49 a harin bindigar da ya kai wani gidan rawa na ‘yan luwadi da madigo a Orlando.

You may also like