An kai harin a kan jirgin kasa a Switzerland


Wani ya kai hari da wuka da wuta a kan fasinjoji a cikin jirgin kasa a Switzerland

Wani mutun ya kai hari a cikin jirgin kasa dauke da ke da fasinjoji a kasar Switzerland, mutane shida ciki har da wani yaro mai shekaru shida suka samu munanan raunuka ta hanyar konewa da yankan wuka. Jami’an ‘yan sanda da ke yankin St Gallen sun ce mutumin ya tada wuta a cikin jirgin yayin da ya yayyanka wasu da wukar da ke hannunsa.

Kawo yanzu dai, babu wasu cikakkun bayanan a kan maharin da ma dalilansa na kai harin to sai dai an kai ga tantance shekarunsa 27 ne kuma dan asalin kasar ta Switzerland.

You may also like