An kai harin kunar bakin wake a wajen bikin aure a Iraki


 

 

An kai harin kunar bakin wake a wajen taron bikin aure a Iraki makamancin wanda aka kai a ranar 20 ga watan Agustan 2016 a garin Gazientep na Turkiyya.

An kai harin ne a kudancin Baghdad babban birnin kasar ta Iraki  inda rahotannin farko suka ce mutane 15 sun rasa rayukansu.

Rahotanni sun ce, mutane 15 kuma sun mutu sakamakon ahrin da aka kai da bam da aka samar da hannu.

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce, maharan su 5 ne kuma daya daga cikinsu ya kashe kansa tare da jama’a inda jami’an tsaro suka kashe wasu 3 inda daya daga cikinsu kuma ya samu nasarar guduwa.

Maharan sun saka kayan soji da kuma na farar hula.

You may also like